TAUSAYIN QASSEM SOLEIMANI GA AL’UMMA DA TAIMAKONSA GA MUTANE
Haj qassem soleimani mutum ne me taimako da kuma tausasawa ga mutane, haka yana da taimako ga wadanda aka zalunta.
Idan kana ganin yanda wannan shahid ya rayu zakasha mamaki domin yanda yake taimakawa al’umma, dakuma yanda yake taimakon wadanda aka zalunta.
Haj qassem yana da hotuna da videos wadanda aka nunashi shida mutanen da da’ish suke zalunta, yana tausaya masu ya rungume su yana karfafarsu hade da basu hakuri bisa irin yanda da’ish ta lalata masu muhallansu, yakasance yana yawan fara’a ga yara da manya sannan yana da son yin kyauta.
Wannan shahid yana da kishin mutane palastine, ta yanda yake taimakonsu yana karesu daga sharrin yahudawan isra’el wadanda suka mamaye palestine suke zaluntar al’ummar palestine.
Sabida taimakonsa yara kananu suke yawan son zama dashi da yawan hira dashi, sannan yana yawan sakar masu fuska da tausayi agare su.
Haj qassem yazama garkuwa ga mutane palastine haka yazama garkuwa ga mutanen syria da Iraq, domin ya hana america da isra’el su zalunce su. Baya son zalunci sam kuma baya shiri da azzalumi, sannan baya tsoron azzalaumi.
Shi azzalumai ne suke tsoronsa domin baya raga masu kwata-kwata, domin ko sunanshi aka ambata azzalumai hankalinsu tashi yake domin irin yanda yake yaki da zaluncinsu.