IRIN NASARAR QASEM SOLEIMANI DA ABU MAHDI ALMUHANDIS SUKA SAMU.
Wadannan mutane ko shakka babu tarihi yayi tasjilin(rubuta) irin ayyukan da sukayi sannan sunayensu sun zama daga cikin sunayen gwarazan da suka firgita azzalumai da masu goya masu baya.
Wadannan jarumai tare da yan rakiyar su, da sukai shahada atare sun samu babbar nasara ta samun shahada, wanda dama ita shahada sai wanda Allah (s.w.t) ya zaba, sannan yake iya samu. Sannan yana daga abun da yake shima nasara ce agaresu shine, soyayyar da suka samu a dunia daga wajan al’ummomi da dama.
Yana daga nasara da haj qassem soleimani ya samu shine, ba kawai jarumin iran ya zama ba, aa ya zama jarumi ne na duk duniya gaba daya, ta yanda ko yaushe rubutu ake game dashi, sunansa da jarumtarsa kara yaduwa suke a duniya gaba daya.
Taimakon raunana da wadanda ake zalunta shine babban akin da wannan jarumai suka gabatar sun taimaki al’ummar palastine da yemen da syria da kuma iraq, kuma duk wannan aiki sunyi shine cikin iklasi da neman yardar Allah (s.w.t) wannan nasarace babba wacce tarihi bazai manta da ita ba.
Haj qasem mutum ne me halaye masu kyau da sallamawa ga Jagoran juyin juya hali a Iran Ayatullahi Ali khamna’e Allah ya kara mashi tsawon rai.
Sirrin nasarar haj qassem shine tausayinsa da irin yanda yaje jajurcewa a yayin gudanar da ayyukansa