GWAGWARMAYAR ABU MAHDI ALMUNDIS DA QASSEM SOLEIMANI
Daga cikin hanyoyin da kafuran dunia makiya musulunci suka kirkiro wajen ganin bayan kasashen musulunci shine kirkira da samar da ”yanta’adda wadanda zaku rika cikawa yahudawan duniya burinsu na ganin bayan kasashen musulunci.
Su wadannan kafurai na dunia ba kowacce kasa ta musulunci suke yaka ba, sai kasar da takasance bata masu biyayya bata kuma hada kai dasu wajan yada fasadi da zalunci.
Tunda dadewa kafuran duniya suka mallaki kasar saudi arebiya ta hanyar mallakar shuwagabannin kasar, sune kuma suke juya kasar da kuma tsara abubuwan mulki a wannan kasa ta saudiyya, hakanne yasa sune suke sanya sarki sune kuma suke ayyana magajin sarki a wannan kasa ta saudiyya.
Sabanin kasar Iran wacce a yanzu itace kasa guda daya ta musulunci wacce sojan america bashi da ikon shigowa ciki, haka kuma sun wadatu da duk wani abu nasu, basa kuma shakkar mayarwa da yahudawa da amurkawa raddi a duk lokacin da suka taba musulunci da al’ummar musulmai.
Gwagwarmar shahid qassem soleimani da Abu mahdi almuhandis itace tahana yahudawa da amurkawa ikon mamaye kasashen musulunci da basa biyayya ga america da isra’el, kuma wadannan jarumai guda da sojojin dake aiki a kasansu, sune suka hana kafuran duniya mallakar yankin asia.
………..Abu zahra……….